14 Nuwamba 2021 - 11:38
​MDD Ta Ce Har Yanzu Ana Tsare Da Ma’aikatanta 9 Da Direbobi 70 A Kasar Habasha

MDD ta bada sanarwan cewa har yanzun ana tsare da ma’aikatanta 9 da kuma direbobi 70 wadanda yakamata su kai kayakin agaji na majalisar zuwa yankin Tigray na arewacin kasar Habasha, ba tare da bayyana wani dalili na yin haka ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Egypt daily ta kasar Masar ta nakalto kakakin majalisar Stephane Dujarric ya na fadawa ‘yan jarida kan cewa mutane a yankin Tigray su na mutuwa saboda karancin abinci da magunguna, sannan duk kokarin da majalisar tayi na isar da kayakin agaji zuwa yankin gwamnatin tsakiyar kasar ta Habasha ta hana.

Labarin ya kara da cewa har yanzun gwamnatin kasar ba ta bada wani bayani ko dalilin na ci gaba da tsare ma’aikatanta 9 da kuma direbibo 70 wadanda majalisar ta dauka don kai kayakin agaji zuwa yankin na Tigray ba.

Har’ila yau shugaban kungiyar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyanawa ‘yan jaridu a birnin Geneva Helkwatan hukumar kan cewa ana fama da karancin magunguna mai tsanani a yankin na Tigray amma har yanzun babu damar shiga yankin.

A wani labarin kuma saketarin harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken yay i kira ga bangarorin da suke rigima a tsakaninsu a kasar na Habasha da su zauna kan teburin tattaunawa don kawo karshen halin da ake ciki a yankin na Tigray.

342/